Daya daga cikin ginshikan tsarin dimokuradiyya shi ne zabi – bai wa jama’a dama su zabi abin da suke so, ko kuma wanda suke so ya shugabance su.
Wannan ne ya sa daya daga cikin muhimman matakai a kafuwar tsarin shi ne zabe.
Sai dai kuma abin tambaya shi ne, zabin ya hada har da na yin zabe ko kaurace masa?
Mene ne matsayin tsarin dimokuardiyya idan aka wajabta wa al’umma kada kuri’a?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba.