Kula da lafiya na nufin yin abubuwa da ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa jiki na aiki yadda ya kamata.
Wannan ya haɗa da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, da dai sauran su.
Sai dai a wannan zamani ‘yan Najeriya ba kasafai suke kula da lafiyar jikin su ba, a mafi yawan lokuta ma sai ciwo ya kwantar da mutum sannan yake tunawa da likita.
Ko wadanne matakai ya kamata 'yan Najeriya su ringa dauka wajen kare kan su da ma lafiyar jikin su?
Shirin Najeriya A YAU na wannan lokaci zai yi nazari ne kan yadda 'yan Najeriya zasu dinga kula da lafiyar jikin su.