Mene ne ya sa jiga-jigan ’yan siyasar Najeriya bangaren adawa suka zabi inuwar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) don hada hannu da nufin kawar da Shugaban Kasa Bola Tinubu da APC dagga mulki?
Da daren Talata ne dai jigogin adawar, wadanda suka hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai da kuma dan takarar Shugaban Kasa na Labour Party a 2023, Peter Obi, suka yanke shawarar tsugunawa a karkashin inuwar ADC din.
Shin ko wannan jam’iyya tana da inuwa mai ni’imar da za ta iya rike wannan hadaka? Shin wadannan ’yan siyasa za su iya ci gaba da shan hannu da juna har su kawar da gwamnati mai ci?
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai nazari ne kan karfin da wannan kawance yake da shi na kalubalantar gwamnati mai ci.