Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa
Jun 02, 2025
Idris Ɗaiyab Bature

Send us a text

Shin wanne ya fi zafi – takaicin rasa matsuguni ko alhinin Rashin sanin halin da dan uwa na jini yake ciki?


Wannan ne halin da wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja suke ciki, bayan da suka tsinci kansu tsamo-tsamo a tsakiyar wata mummunar ambaliyar ruwa.
Wasu mutanen da dama dai sun yi batan dabo a wannan ibitila’i, wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutanen da adadinsu ya haura 150.


Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda wadannan dubban mutane suka kai labari da halin da suke ciki.