Wata dabi’a da ta zama ruwar dare ita ce yadda matasa suke yankawa suke kuma da fige kaji a unguwanni, musamman a lokutan shagulgulan sallah.
A da can akwai kebabbun wurare da ake gudanar da irin wadannan abubuwa.
Sai dai masana suna ganin hakan na tafe da illolin kiwon lafiya da ma gurbata muhalli.
Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai yayin da ake bikin Ranar Muhalli ta Duniya kwana guda kafin Babbar Sallah.