Abubuwan Da Suka Fara Bacewa Yayin Bukukuwan Sallah

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Abubuwan Da Suka Fara Bacewa Yayin Bukukuwan Sallah
Jun 06, 2025
Idris Ɗaiyab Bature

Send us a text

Yau mutane na kallon bukukuwan Sallah da ido daban—yayin da wasu ke ganin ta zama lokaci na shakatawa nishadi kawai, wasu kuwa na cewa an bar al’adun da ke nuna kimar wannan babban lokaci na Musuluncin.


Wadanda suka manyanta na ganin akwai abubuwa da dama da a yanzu matasa sukayi watsi da su wadanda kuma na da muhimmanci yayin bukukuwan sallah a da can baya wanda kuma suke ganin ba a yin su a yanzu.
Ko wadanne irin al’adu kenan na bukuwan sallah da dattawa ke ganin anyi watsi dasu.


Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan yadda aladun bukukuwan Sallah ke canzawa a wannan zamani.