Sabbin masu sana’oi na tafka kurarai da suka hada da rashin kyakkyawar tsari, karancin jari, rashin shawarwarin kwararru da wasu kalubalen na daban.
Sai dai masana suna ganin idan sabbin masu sana’oi za su yi amfani da shawarwarin da suke badawa zai taimaka wajen dorewar sabbin sana’oin su.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin wadannan kura-kurai da kuma shawarwarin da masana suka bada don dorewar sabbin sana’oi.