Halin Da Alummar Mokwa Ke Ciki Wata Guda Bayan Ambaliya

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Halin Da Alummar Mokwa Ke Ciki Wata Guda Bayan Ambaliya
Jul 01, 2025
Idris Daiyab Bature

Send us a text

Tun bayan da ambaliyan ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa ne dai alummar garin suka fada halin neman taimako.

A yayin da gwamnatin tarayya da ma wasu daidakun mutane suka taimaka ma wadanda abun ya shafa da kudi da ma wasu kayayyakin masarufi, wasu daga cikin alummar sun bayyana rashin jin dadin su ga yadda alamura ke gudana a garin Mokwa.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai nazari ne kan halin da alummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliyar ruwan da ci wasu sassan na garin.