Tun kafin sanar da sabuwar kawance da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El’rufai da wasu manyan ‘yan siyasa ne aka fara zargin yiwa wannan hadaka zagon kasa da kawo cikas ga tafiyar wannan hadaka.
Daya daga cikin irin wadannan zagon kasa da ake zargin wasu da yiwa wannan sabuwar hadaka itace na sanar dasu rashin samun dakin taron da suka shirya gudanar da taron lokaci kalilan gabanin taron.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan boyayyun kalubalen da sabon hadakar jamiyyar ADC zata iya fuskanta gabanin 2027.