Yan Najeriya da dama na ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan sabon hadakar ‘yan siyasa zuwa sabuwar jami’yyar ADC.
A yayin da wasu ke ganin wannan hadaka za ta cire musu kitse daga wuta, wasu kuwa gani suke yi duk kanwar ja ce.
A ranar laraban nan ne dai gaggan ‘yan siyasa daga jamiyyu daban daban suka hadu don dinkewa wuri daya da niyyar kalubalantar jamiyya mai mulki ta APC, a cewar su za su ceto Najeriya daga halin da jamiyyar ta jefa su a ciki.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan ko sabuwar hadakar jamiyyar ADC za ta fidda ‘yan Najeriya daga matsalar da suka ce suna ciki?