'Yan Najeriya suna ci gaba da tafka muhawara a kan wanda jamiyyar hadaka ta ADC zata tsayar takarar Shugaban Kasa a zaben 2027.
Yayin da wasu suke ganin Atiku Abubakar yana da dimbin magoya baya, wasu kuwa gani suke yi shi ma Peter Obi ba kanwar lasa bane.
Ko me zai faru idan daya daga cikin su ya samu tikitin tsayawa takara a 2027?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan wannan lamari.