Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya.
Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata.