Zagon kasa da wasu ‘ya’yan PDP ke yi mata na kara ta’azzara, inda wasu ke zama a cikin ta amma suke wa jam’iyyun adawa aiki.
Ko a kwanan nan, an hangi wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar a taron hadakar ADC, wadda hakan ke jaddada har yanzu PDP ta kasa kawo karshen wannan matsala.
Ko me yasa ‘ya’yan PDP ke yiwa jam’iyyun adawa aiki?
Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.