Tashin farashin takin zamani yana hana manoma da dama noman wasu nau’ukan abinci.
Manoma da dama dai suna kauracewa shukan masara da shinkafa da aka fi amfani da su a Najeriya sakamakon tsadar takin zamani, inda masana suke ganin in ba’a dauki mataki ba hakan zai kawo karancin abinci a Najeriya.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa farashin takin zamani yayi tashin gwauron zabi a Najeriya.