‘Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana basa fitowa kada kuri’a a duk lokacin da zabe ya zagayo.
Wasu daga cikin ‘yan Najeriya sun bayyana dalilan su da suka hada da rashin jin dadin abun da hukumar zabe keyi, rashin yadda da sakamakon zabannin da suka gabata da dai sauran su a matsayin dalilan su.
Ko wadanne matakai hukumar zabe INEC take dauka don karfafawa ‘yan Najeriya gwiwan fitowa kada kuri’a a 2027?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.