Halin Kunci Da Wadanda Hare-haren Ta'addanci Ya Rutsa Da Su Ke Ciki

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Halin Kunci Da Wadanda Hare-haren Ta'addanci Ya Rutsa Da Su Ke Ciki
Aug 21, 2025
Idris Daiyab Bature

Send us Fan Mail

A yau, ta’addanci ya zama babban kalubale ga tsaron rayuka da dukiyoyi, ya raba iyalai, ya tilasta dubban mutane barin gidajensu, ya hana yara zuwa makaranta, kuma ya durƙusar da tattalin arzikin yankuna da dama. 


Baya ga haka, ta’addanci ya bar raunuka masu zurfi na damuwa da tsoro a zukatan waɗanda suka tsira, wanda sau da yawa ba sa samun kulawar kwararru.


Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan yadda hare-haren ta’addanci ya shafi rayuwar alumma da dama.