Me Sakamakon Zaben Ribas Ke Nunawa Game Da Sulhun Wike Da Fubara?

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Me Sakamakon Zaben Ribas Ke Nunawa Game Da Sulhun Wike Da Fubara?
Sep 01, 2025
Idris Daiyab Bature

Send us Fan Mail

Yadda Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, da magoya bayansa suka kaurace wa zaben kananan hukumomin jihar, da yadda APC ta lashe kujeru 20 a cikin 23 sun haifar da muhawara a tsakanin ’yan Najeriya.


Shin wannan sakamako alama ce ta yarjejeniyar sulhu da aka cimma a tsakanin Gwamna Fubara da Minsitan Abuja Nyesom Wike a Fadar SHugaban Kasa?


Amsar wannan tambaya shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci za iyi yunkurin bicikowa.