Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
Sep 16, 2025
Idris Daiyab Bature

Send us Fan Mail

Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar.


Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata.


Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu.