Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki
Nov 20, 2025
Idris Daiyab Bature

Send us Fan Mail

Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu.


Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su.


Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin halin da irin wadannan mata ke shiga da kuma hanyoyin da zasu bi don dawo da martaba a rayuwarsu.