Murabus din da Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai ta kasa Ahmed Farukh ya yi daga mukaminsa ya sa ‘yan Najeriya da dama na ta tofa albarkacin bakinsu musamman a bangaren harkokin mai.
Murabus din na zuwa ne bayan doguwar takaddama tsakaninsa da Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote kan batutuwa da dama.
Shin ko wanne darasi za a koya daga wannan takaddama da ta kai ga murabus din shugaban.
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.