‘Yan kasuwa da dama a jihar Kano sun kwana sun tashi da juyayi da alhinin gobara da ta faru ta kuma lashe musu dimbin dukiyarsu suna ji suna gani ba tare da sun iya tabuka komai ba.
Gobarar da ta tashi a kasuwar singa dake jihar Kano, ta fara ne da misalin karfe 4:30 na ranar asabar ta kuma cigaba da ci har zuwa wayewar garin ranar lahadi. Wannan gobara ta yi sanadiyyar raba ‘yan kasuwa da dama da hanyar cin abincin su, inda ta jefa su da iyalansu cikin halin kunci.
Ko wanne irin hasara wadannan ‘yan kasuwa suka tafka sakamakon wannan gobara?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.