Kalubalen Dake Tattare Da Samar Da ‘Yansandan Jihohi A Najeriya

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Kalubalen Dake Tattare Da Samar Da ‘Yansandan Jihohi A Najeriya
Mar 06, 2026
Idris Daiyab Bature

Send us Fan Mail

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sha nanata muhimmancin samar da ’yan sandan jihohi a Nigeria, yana mai cewa hakan na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na kasar. Shugaban ya bayyana cewa tsarin ’yan sanda da ke karkashin gwamnatin tarayya kadai ba zai iya biyan bukatun tsaro na kasa mai yawan jama’a da fadi kamar Najeriya ba.


A wani mataki na ci gaba da duba yiwuwar aiwatar da wannan tsari, Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Tunji Disu, jim kadan bayan kama aikinsa ne ya kafa wani kwamiti na musamman domin nazartar hanyoyin da za a bi wajen samar da ’yan sandan jihohi.

Sai dai duk da yadda wasu ke ganin cewa kafa ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen inganta tsaro, masana da masu ruwa da tsaki na cewa akwai kalubale da dama da ka iya tasowa.


Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin kalubalen da shirin samar da ‘yansandan jihohi zai iya fuskanta.