
Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Podcasting since 2021 • 204 episodes
Daga Laraba
Latest Episodes
Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa
Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika daya.Masu kananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da k...
•
26:11

Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko ‘ya riƙo. A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu.Wannan alada ana yin ...
•
23:01

Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’
Tun kaka da kakanni an san Hausawa da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su.Mai yiwuwa wadannan dabi’u ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka.To amma a zamani...
•
23:51

Dalilan Zuwan Mafarautan Arewa Kudancin Kasar Nan
Tun bayan kisan mafarauta 16 dake hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi dake karamar hukumar Esan dake jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi...
•
30:11
