
Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Episodes
204 episodes
Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa
Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika daya.Masu kananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da k...
•
26:11

Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko ‘ya riƙo. A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu.Wannan alada ana yin ...
•
23:01

Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’
Tun kaka da kakanni an san Hausawa da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su.Mai yiwuwa wadannan dabi’u ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka.To amma a zamani...
•
23:51

Dalilan Zuwan Mafarautan Arewa Kudancin Kasar Nan
Tun bayan kisan mafarauta 16 dake hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi dake karamar hukumar Esan dake jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi...
•
30:11

Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin Sallah
A duk lokacin da aka ce lokutan bukukuwa sun karato, akan samu sauyi a dukkan alamura.Daya daga cikin irin wadannan sauyi da ake samu shine na farashin kayayyakin masarufi. A wasu lokuta, akan samu tashin farashin ...
•
26:36

Abin Da Kundin Tsarin Mulki Ya Ce A Kan Ayyana Dokar Ta Ɓaci
A karshe dai hasashen da wasu ke yi a Ribas ya tabbata, inda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci, ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa, da ma ''yan majalisar dokokin jihar.Sai dai bayan ayyana wannan d...
•
27:18

Ko Kun San Asalin Tashe Da Tarihinsa A Kasar Hausa?
Bayan dunbum falala, da yawan samuwar ibadun dake kara kusanta bayi ga ubangijin su, da azumin watan ramadana ke zuwa dashi kamar yadda malamai suka saba fada mana, Hakazalika Kuma a watan na Ramadan dai na zuwa da wata alada mai dimbin tarihi ...
•
27:42

Yadda Zawarawa Suke Dandana Kuda A Watan Ramadana
Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta.Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale – ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza shiryawa.Wani rukunin wadannan muta...
•
31:09

Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa
A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”.A al’adance, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu maz...
•
23:12

Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi?
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade.Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwa...
•
22:33

Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa
Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa.Sai dai wannan dadaddiyar al’ada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba.Shirin Daga Larab...
•
29:44

Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma 'Event Centre'
A da akan kwashe kwanaki ana bukuwan aure a kasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin bik da zaman ajo zuwa budar kai da sayen baki.Sai dai wadannan al’adu sannu a hankali suna ta gushewa.Ko mene ne dalilin wannan sauyin?...
•
29:48

Dalilan Da Suka Sa Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata
Son haihuwar ‘ya’ya maza fiye da ‘ya’ya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin alummomi daban-daban.A tsakanin wasu al’ummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cik...
•
29:49

Me Ya Sa Matasa Ba Sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana'a?
Samun ingattattun malamai a makarantun firamare da sakandare na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tubalin ingantaccen kuma nagartaccen ilimi a cikin al’umma.Ɗorewar wannan fafutuka ta samar da ingantaccen ilimi kuma ta dogara ne a kan...
•
26:56

Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko 'ya riƙo. A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu.Wannan alada ana yin ...
•
23:01

Yadda Sunayen Zamani Suke Neman Kawar Da Na Hausawa
A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaka da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauran su.Sai dai yayin da a da sunayen da Hausawa kan sanya wa ’ya’yansu na Annabawa k...
•
28:27

Dalilan Da Suka Sa Matan Wannan Zamanin Ba Sa Son Talaka
A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa.Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai hannu da shuni ya fito takan tubure...
•
27:46

Dalilan Da Suka Sa Wasu Darikun Kirista Basa Bikin Kirsimeti
A dukkan kwanakin karshen watan Disambar kowace shekara, lokacin ne da farin ciki ke cika a fuskokin Mabiya Yesu Almasihu don gudanar da bukuwaN ranar tunawa da haihuwar sa wato kirsimeti.Sai dai, wasu darikun addinin kirista da suka ha...
•
27:33

Yadda Shara Ke Neman Binne Manyan Biranen Najeriya
Tururuwar da mutane suke yi zuwa manyan biranen Najeriya na barazana ga wadannan alƙaryu ta fuskar tsaftar muhalli.Misali, wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa a duk sa'a daya birnin Legas kan yi baƙi 77 ...
•
27:44

Me Nasarar Da John Mahama Ya Samu Ke Nufi Ga kasar Ghana
A karshe dai an ayyana John Mahama a matsayin zababben shugaban kasar Ghana bayan da al’ummar kasar sun yanke shawarar zabensa lokacin da suka kada kuri’a ranar Asabar din da ta gabata.Duk da sauran ‘yan Takara da John Mahama ya kara da...
•
29:52

Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Kishin Kabila Fiye Da Kasa
Kishin kasa na cikin abubuwan da shugabanni, da sauran masu ruwa da tsaki suke kira ga ’yan Najeriya a kullum a kansu.Muhimmancin kishin kasa ga cigaban al’umma, musamman a kasa mai kabilu da addinai daban-daban irin Najeriya, abu ne da...
•
31:41

Gudunmawar Da ‘Yan Sa Kai Suke Badawa Wajen Yaki Da Matsalar Tsaro
Matsalar tsaro na daga cikin batutuwan da suka hana kasar nan cikas a ‘yan shekarun nan.Kuma kamar yadda alumma ke bayyanawa akwai karancin jami’an tsaro da ya kamata ace suna lura, tare da kiyaye rayuka da dukiyoyin alumma a koda yaushe...
•
30:16

Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya A Najeriya
An daɗe ana muhawara, musamman a Arewacin Najeriya, a kan buƙatar yin garambawul ga tsarin makarantun tsangaya.A baya dai waɗannan makarantu kan samar da mahaddata alqur’ani waɗanda kuma sukan dogara da kaiSai dai a wannan zamani, y...
•
24:57
