Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Abin Da Ya Sa Kotu Ta Tsige Gwamnonin Arewa Huɗu
•
Aminiya
Bayan watanni tara da kammala zaben 2023 da zubar da wasu jiga-jigan yan siyasa, bangaren shari’a ma na cigaba da zartar da hukunci, inda zuwa yanzu aka tsige akalla gwamnoni hudu daga jam’iyyu daban-daban.
Wasu na ɗiga ayar tambaya kan saƙaƙiyar da alƙalai ke amfani da su wajen yanke hukunci a kotunan.
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba ainihin dalilan da suka sa kotunan tsige gwamnonin huɗu zuwa yanzu.