Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Mahimmancin Barin Wasiyya Tun Kana Da Rai
•
Aminiya
Da zarar an ambaci wasiyya sai mutum ya fara tunanin mutuwa, ko wani abun na daban a rai.
Wasu kan bar wasiyya ko da za su yi tafiya zuwa anguwa saboda gudun riskar wa'adi a lokacin da ba shiri. Shin ya mahimmancin wasiyya take da kuma tasirin hakan?
Ku biyo mu shirin Daga Laraba na wannan makon domin jin mahimmancin barin wasiyya tun mutum na raye.