Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Matakan Kariya Daga Kwantawa Rashin Lafiya
•
Aminiya
Lafiya dai ita ce uwar jiki, babu mai fushi da ita. A yanayin da aka ciki babu mai son ya ga ya kwanta rashin lafiya, domin ana lallaba halin da ake ciki.
Jama’a na kokawa a fannoni da dama yayinda wasu kyale batun ziyartar asibiti ko shan magani ko da sun ji alamar canji a jikinsu.
Ku kasance da shirin Daga Laraba na wannan mako domin wasu dabarun da za su taimaka wajen ganin ba ku kwanta rashin lafiya ba.