
Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Yadda ‘Yan Arewa Za Su Samu Kuɗi A Soshiyal Midiya
•
Aminiya
Kafafen sada zumunta sun zama farfajiyar baje kolin basira, yayin da ta kan zame musu hanyar bayyana damuwa da share kokensu.
Ana yawan buga misali da cewa an yiwa yankin Arewacin Najeriya nisa wajen samun tagomashin a soshiyal midiya.
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba dabarun da masu amfani da shafukan za su bi wajen ganin sun amfana yadda ya kamata.