Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
"Ruwan 'Fiyowata' Na Neman Ya Gagari Talaka"
•
Aminiya
Tsadar rayuwa ta sa ruwan leda wato 'fiyowata' ya fara zama abin tattaunawa gameda yadda yake tsada.
Wasu na ganin shine ruwan da ake samu mai dama-dama wajen tsafta idan mutum na so ya sha ruwa, sai dai yadda yake kara tsada a sassa daban-daban na Najeriya ya sa ana komawa shan ruwa mara tsafta a wasu wuraren.
Sai dai masu sarrafa ruwan na cewa ba daga su ba ne, inda har ta kai ga wasu na rufe kamfanoninsu.
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba dalilin da suka jawo hakan.