Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Me Ya Sa Kamfanonin Lantarki Suke Fifita ‘Yan ‘Band A’?
•
Aminiya
Bayan komawa tsarin rukuni daban-daban na bayar da wutar lantarki Idan kamfanoni na neman afuwa to yawancin ga ‘yan rukunin farko ne.
Wasu na ji a ransu kamar su ba kwastomomi bane ga kamfanonin domin kulawar da ake ba su ta nuna ba a tare da su.
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da ya sa hankalin kamfanonin wutar lantarki ya karkata wani fanni.