Daga Laraba

Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko 'ya riƙo. 

A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu.
Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauƙaƙa danƙon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu. 

Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan matsalar ’ya’ya da iyayen riko.