Daga Laraba

Me Ya Sa Matasa Ba Sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana'a?

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Samun ingattattun malamai a makarantun firamare da sakandare na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tubalin ingantaccen kuma nagartaccen ilimi a cikin al’umma.

Ɗorewar wannan fafutuka ta samar da ingantaccen ilimi kuma ta dogara ne a kan samun haziƙan matasa da za su maye gurbin malaman da ake da su yanzu. 

Sai dai a Najeriya, alamu  suna nuni da yadda matasa da dama suke gudun aikin koyarwa, musamman a kananan makarantu.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari a kan dalilan da suka sa haka.