
Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma 'Event Centre'
•
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
A da akan kwashe kwanaki ana bukuwan aure a kasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin bik da zaman ajo zuwa budar kai da sayen baki.
Sai dai wadannan al’adu sannu a hankali suna ta gushewa.
Ko mene ne dalilin wannan sauyin?
Wannan ne batun da shirin Daga Laraba zai duba a wannan makon.