Daga Laraba

Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa.


Sai dai wannan dadaddiyar al’ada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba.


Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan wannan al’ada da kuma dalilin gushewar ta.