
Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Ko Kun San Asalin Tashe Da Tarihinsa A Kasar Hausa?
Bayan dunbum falala, da yawan samuwar ibadun dake kara kusanta bayi ga ubangijin su, da azumin watan ramadana ke zuwa dashi kamar yadda malamai suka saba fada mana, Hakazalika Kuma a watan na Ramadan dai na zuwa da wata alada mai dimbin tarihi dake debe wa alumma musamman na arewacin Najeriya kewa.
Wannan aladar itace ta tashe da ake fara yinta da Zarar watan azumi ya kai kwanaki goma.
Maza da mata na gudanar da wannan alada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da bat da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo kwararo dauke da ganga da kayan kade kade suna bugawa suna waka.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan wannan dadaddiyar aladar, don jin inda ta samo asali, tarihin ta, da kuma yadda ake Gudanar da ita.