
Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Abin Da Kundin Tsarin Mulki Ya Ce A Kan Ayyana Dokar Ta Ɓaci
A karshe dai hasashen da wasu ke yi a Ribas ya tabbata, inda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci, ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa, da ma ''yan majalisar dokokin jihar.
Sai dai bayan ayyana wannan doka da shugaban kasar ya yi 'yan Najeriya da dama suna ta bayyana ra’ayoyinsu kan wannan lamari.
Yayin da wasu suke cewa tuni ya kamata Shugaban Kasar ya dauki wannan mataki, wasu kuwa cewa suke yi ba shi da hurumin dakatar da zababben gwamna.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan ko Doka ta bai wa Shugaban Kasa ikon dakatar da gwamnan jiha da ma 'yan majalisar dokokinta?