
Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Dalilan Zuwan Mafarautan Arewa Kudancin Kasar Nan
Tun bayan kisan mafarauta 16 dake hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi dake karamar hukumar Esan dake jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu.
A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na ‘yan kasa masu cikakken ‘yanci, suna da damar kutsawa lungu da saƙo na ko ina a fadin kasar nan, wasu kuwa tambaya suke shin me ya kai ‘yan Arewa har kudancin kasar nan don yin farauta?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa mafarautan arewa zuwa kudancin Najeriya yin farauta.