
Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa
•
Idris Daiyab Bature
Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika daya.
Masu kananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durkushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taba rayuwar al’umma da hanyoyin magance ta.