
Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah
Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda suka jibanci bikin sallah.
Siyayyan kayan kayan abinci na daya daga cikin wadannan hidindimu, sai dai kayan miya da suka zama dole ayi amfani dasu yayin bikin sallah sun yi tashin gwauron zabo inda alumma da dama ke ta bayyana damuwar su kan wannan batu.
shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa farashin kayan miya suka yi tashin gwauron zabo gabanin bikin Sallah.