
Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Abubuwan Da Ya Kamata Yara Su Yi Yayin Hutun Makaranta
•
Idris Daiyab Bature
A duk lokacin da akace an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abu na dabam da kuma basu damar shakuwa da ‘yan uwa da abokan arziki.
Kamar yadda masana harkar masana harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da nashi irin matsalolin, ya kuma kamata ace ana warewa dalibai wasu lokuta na musamman don samun hutu daga karatun da suka koya.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan abubuwan da ya kamata yara su ringa yi yayin hutun makaranta.