Daga Laraba

Dalilan Alummomi Na Rungumar Gwaji Kafin Aure

Idris Daiyab Bature

Wasu alummomi sun bayyana dalilan da suka sa suka karbi gwajin ma’aurata kafin a daura musu aure.


A wasu lokutan akan samu matsaloli sakamakon rashin gwajin jini kafin a hada mace da na miji aure da suka hada da yaduwar cutuka, samun ‘ya’ya marasa lafiya da sauran wasu matsalolin.


Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu alummomin suka rungumi gwajin jini kafin aure.