Daga Laraba

Yadda wasu tsare-tsaren ba da tazarar haihuwa ke yin illa ga mata

Idris Daiyab Bature

A kokarin iyaye mata na kula da lafiyarsu da kuma tsare lafiyar iyalansu, hanyoyin bada tazarar haihuwa na asibiti sun zama zabin da dama ke komawa gare su. 


Sai dai duk da shaharar wadannan hanyoyi, akwai mata da dama da ke fuskantar matsaloli daban-daban yayin amfani da su. 

Wasu na fama da illa ta jiki kamar zubar jini fiye da kima, ciwon mara ko canjin yanayin jini, yayin da wasu kuma ke fama da matsaloli na tunani saboda tsoron illar hanyoyin ko rashin samun isasshen bayani daga ma’aikatan lafiya. 


Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan nau’ukan tazarar haihuwa da ya kamata mata su rika amfani da su.