Daga Laraba

Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027

Idris Daiyab Bature

Karuwar hare-hare kan ’yan siyasa a kwanan nan ta sa wasu ’yan Najeriya sun fara fargabar abin da ka iya faruwa idan aka fara yakin neman zaben 2027.


A kwanan nan ne dai wasu wadanda ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai hare-hare a kan tarurruka ko kadarorin jam’iyyu ko ma daidaikun ’yan siyasa.


Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda siyasar 2027 za ta kasance duba da yadda hali yake a yanzu.