Daga Laraba

Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku

Idris Daiyab Bature

Sau da dama mukan ji labarai na mutane da suka ɗauki rayukansu saboda damuwa, talauci ko kuma rashin samun mafita a cikin rayuwa. 


A cikin wannan shirin, za mu kalli batun kisan kai daga wani ɓangare na daban, ba wai kawai daga alkaluma ba, amma ta hanyar jin labarin wani da ya taɓa  yunkurin kashe kansa har sau uku. 


ko wadanne irin matsaloli ne suka tunzura wannan bawan Allahn yunkurin daukar ransa da kansa har sau uku?