Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Daga Laraba
Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
•
Idris Daiyab Bature
A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani.
Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa.
wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba akai.