Daga Laraba

Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata

Idris Daiyab Bature

Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya.

 

Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi  ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya.

 

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata.