Daga Laraba

Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai

Idris Daiyab Bature

Tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960, Najeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Amma tun daga wannan lokaci, al’ummar Najeriya sun kasance cike da bambance-bambancen addini da kabila da harshe da al’adu da kuma ra’ayin siyasa. Wadannan bambance-bambancen sun kasance ginshiki guda biyu: a wani lokaci suna zama jigo wajen gina ƙasa mai cike da nishaɗi da ɗimbin albarkatu, wani lokaci kuma suna haifar da tangarda wajen tafiyar da ci gaban ƙasa.


Bayan shekaru 65 da samun ’yancin kai, ana iya cewa bambance-bambancen da ke tsakanin ’yan Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasar, amma kuma sun bar gibi a fannin haɗin kai da kwanciyar hankali da samar da ci gaba. 


wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai shekara 65 bayan samun 'yancin kan Najeriya.