Daga Laraba

Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya

Idris Daiyab Bature

Sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, inda ake zargin cewa rikicin ya kai ga hana tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan jam’iyyar a matakin kasa sun nuna adawa da niyyar Lamido na neman kujerar shugabancin PDP, suna ganin cewa ba shi ne ya dace da wannan matsayi a yanzu ba. Sai dai magoya bayan tsohon gwamnan sun bayyana wannan mataki a matsayin nuna son kai da kuma kokarin dakile sabuwar tafiya a cikin jam’iyyar.

Wannan lamari ya sake haska yadda PDP ke ci gaba da fama da rikicin cikin gida, wanda da yawa ke ganin zai iya shafar karfinta da hadinta kafin babban zaben da ke tafe.

Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba a kai.