Daga Laraba

Yadda Ragin Farashin Man Fetur Zai Shafi Rayuwar ‘Yan Najeriya

Idris Daiyab Bature

Rage farashin man fetur a Najeriya na daya daga cikin batutuwan da ke daukar hankalin al’umma, musamman ganin yadda tsadar rayuwa ta yi wa ’yan kasa katutu a ‘yan watannin nan. Man fetur ba wai kawai makamashi ba ne da ake amfani da shi wajen tafiyar da ababen hawa; ginshiki ne da kusan dukkan harkokin tattalin arziki ke jingina da shi – daga sufuri, da samar da kayayyaki, har zuwa rabon su zuwa kasuwanni.


Saboda haka, duk wani sauyi a farashin mai kan yi tasiri kai tsaye ko a kaikaice ga farashin kayan masarufi da ’yan Najeriya ke amfani da su a kullum, kamar abinci, da kayan gini, da magunguna da sauransu. 

Sai dai tambayar da ke yawan fitowa ita ce: shin rage farashin mai zai kai ga rage farashin wadannan kayayyaki? 


Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.