Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Shekara 1 Da Fara Rediyon Aminiya Ta Intanet
•
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed
Yau rediyon Aminiya ta intanet ke cika shekara guda da fara yada shirye-shiyensa.
Daga ranar 19 ga watan Mayun 2021 da muka faro zuwa yau, mun wallafa shirin Najeriya A Yau sau 171 da kuma shirin Daga Laraba guda 53.
Shirin namu na yau ya yi waiwaye ne kan yadda muka faro da kuma ra’ayoyin wadansu masu sauraro kan shirye-shiryen mu.